Abinda Yasa Vincent Enyeama Na Najeriya Ya Zama Golan Da Ya Fi Cin Ƙwallo A Afirka

Dan wasan Najeriya Vincent Enyeama shi ne golan da ya fi zura kwallo a raga a nahiyar Afirka inda ya zura kwallaye 20.

Ya kasance mai bugun fanareti a kulob din Enyimba na Najeriya da kuma kulob din Hapoel Tel Aviv na Isra’ila.

Kenedy Mweene na Zambia shi ne na biyu a jerin wanda ya zura kwallaye 13. Ya kasance mai bugun fanareti a kulob din Free State Stars na Afirka ta Kudu da kuma tawagar kasar Zambia.

Dan wasan Algeria Faouzi Chaouchi, Boubacar Barry na Ivory Coast, Bruce Grobbelaar na Zimbabwe, Yassine Bounou na Morocco, Essam El Hadary na Masar da wasu da dama ne suka zura kwallo daya.