Abinda Yasa Rafari Da Ronaldinho Suka Bushe Da Dariya A Wasan AC Milan Da Inter Milan

A wasa tsakanin AC Milan da Inter Milan, alkalin wasa yaso ya nunawa Ronaldinho katin gargadi (Yellow Card); lokacin da aikata abin da bai dace ba, amma sai alƙalin wasan yayi kuskure ya fitar da jan kati (Red Card).

Da alƙalin wasan ya gane kuskurensa, sai ya maye gurbinsa jan katin da katin gargadin yaso nunawa tun farko, kawai sai suka bushe da dariya.