Wasanni
2014: Dalilin Da Yasa Harry Kane Zama Golan Tottenham A Wasan Su Da Asteras
A wasan gasar cin kofin zakarun Turai (Europa League) ta shekarar 2014 tsakanin Tottenham Hotspur da Asteras Tripolis a White Hart Lane, an kori golan (Goalkeeper) Spurs a minti na 87.
Dan wasan Spurs Harry Kane, wanda ya riga ya zura kwallo 3 a raga a wasan, an tilasta masa zama mai tsaron raga “Emergency Goalkeeper” na sauran mintunan da suka rage, saboda Club ɗin ta yi amfani da dukkan yan wasan da suka sauya (Substitutes).
Sai dai bugun Free Kick na Jeronimo Barrales wanda yasa Asteras Tripolis ta zura kwallo a ragar Spurs.
A ƙarshe Spurs ta lashe wasan da ci 5-1.