2003 – 2006: Tarihin Wasannin Fabian Barthez

Fabian Barthez ya buga wa Faransa wasanni 87, inda ya lashe kofin duniya a shekarar 1998, da Yuro a 2000 da kuma na Confederation a shekarar 2003. Ya kuma kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta 2006.

Shi ne dan wasan da ya fi buga wa Faransa wasa a gasar cin kofin duniya da wasanni 17 kuma tare da Peter Shilton na Ingila, ya ke rike da tarihin wanda ya fi kowa buga wasa a gasar cin kofin duniya (10).

A matakin kulob din ya buga wasa a kungiyoyin Toulouse da Marseille da Monaco da Manchester United da Nantes, inda ya lashe gasar UCL da Marseille a 1992/93 da Premier League da Manchester United a 2000/01 da 2002/03.

Ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa a shekara ta 2007 kuma ya fara aiki a motorsport a shekara mai zuwa.