Wasanni

1989: Yadda Terry Ya Jure Jinin Dake Zuba A Goshin Shi Don Taimakawa Ingila A Wasan Shiga Gasar Cin Kofin Duniya

A wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi tsakanin Ingila da Sweden a shekarar 1989, dan wasan bayan Ingila Terry Butcher ya shiga tsaka mai wuya da dan wasan Sweden Johnny Ekstrom a farkon rabin lokaci, lamarin da ya sa shi zubar da jini.

Bayan an yi masa magani aka daure kan shi da bandeji, sai ya cigaba da wasan. A lokacin cikakken lokaci, farar rigar Butcher ta Ingila tana cike da jini gaba ɗaya.

Wasan dai ya kare ne babu ci kuma ya taimaka wa Ingila samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Italiya ta karbi bakunci a shekarar 1990.