1986: Ko Ka San Morocco Ita Ce Ta Ɗaya A Afirka Da Ta Samu Tikitin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Zagaye Na 16?

A shekarar 1986, Morocco ta zama tawaga ta farko a Afirka da ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na zagaye na 16.

An sanya su a rukunin F, tare da Ingila Poland da Portugal.

Sun lallasa Portugal da ci 3-1, sun yi kunnen doki da Ingila babu ci, sannan suka tashi babu ci da Poland sannan kuma suka tashi a saman rukunin da maki 4.

Sannan kuma sun kara da Jamus ta Yamma a zagaye na 16 inda suka sha kashi da ci 1-0.