1958: Yanda Fontaine Ya Ci Wa Faransa Ƙwallaye 13 A Wasanni 6 A Gasar Cin Kofin Duniya

Just Fontaine ya ci wa Faransa kwallaye 13 a wasanni shida da ya buga a gasar cin kofin duniya a shekarar 1958.

A lokacin (Babu zagaye na 16, wataƙila da ya fi zira kwallaye da yawa).

Babu wani dan wasa da ya zura kwallaye da yawa a gasar cin kofin duniya guda ɗaya.

A matakin rukuni, ya zura kwallaye uku a ragar Paraguay, biyu a kan Yugoslavia, daya a kan Scotland.

A wasan daf da na kusa da na karshe, ya zura kwallaye biyu a ragar Ireland ta Arewa.

A wasan kusa da na karshe, ya zura kwallo daya a ragar Brazil.

A wasan neman matsayi na uku, ya zura kwallaye hudu a ragar Jamus ta Yamma.

Wannan ita ce gasar cin kofin duniya da ya buga. An tilasta masa yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 28 saboda rauni.

Fontaine shi ne na hudu a jerin wadanda suka fi cin kwallaye a gasar cin kofin duniya ta FIFA, bayan Gerd Muller mai (14), Ronaldo de Lima (15) da Miroslav Klose (16).

A halin yanzu yana da shekaru 88 a duniya.