Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa

An samu karin haske kan kisan da aka yi wa hakimin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birnin Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Da yake tabbatar da hakan ga wakilin jaridar Leadership, dan majalisar mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa a majalisar dokokin jihar, Honorabul Almustapha Boza, ya ce tawagar da aka aike domin kai kudin fansa da ‘yan fashin suka nema sun ga gawarsa.

Dan majalisar a wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, ya bayyana cewa tawagar sun dawo ne kawai tare da dansa yayin da tuni aka kashe hakimin gundumar kafin su isa wurin ‘yan bindigar.

“Eh, zan iya tabbatar muku ya mutu, sun kashe shi. Hatta wadanda suka je wajen kai kudin fansa ba su iya haduwa da shi a raye ba, kawai sun dawo ne tare da dansa da aka sace tare da shi, kuma muna kan hanyar mu ta zuwa asibiti a yanzu.”

Idan dai za a iya tunawa, dan majalisar a baya yayin da yake zantawa da wakilin Leadership ya ce, “Mun amince da Naira miliyan 60 da kuma sabbin babura a matsayin kudin fansa. Abin da ya kawo jinkirin isar da kayan shi ne bayanin takamaiman baburan da aka nema wanda aka fi sani da Boko Haram.

“Mun samu babura a yau amma abin takaici ‘yan fashin ba su kira mutumin da suke tattaunawa da shi ba. Suna yawan kira sau biyu a rana; Karfe 8 na safe da 5 na yamma amma yau ba su yi waya ba.”