Wasanni

Ɗan Wasan Da Ya Taɓa Saka Rigar Ƙwallo Mai Lambar Ziro (0) A Tarihi

Hicham Zerouali shine ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa daya tilo da ya taɓa saka lambar riga mai lambar ziro (0) a tarihi.

An yi wa dan wasan Morocco lakabi da “Zero,” wanda aka yi shi daga sunansa, kuma shi yasa ya sanya riga mai lambar (0) a lokacin da yake taka leda a kulob din Aberdeen na Scotland.

A matakin kasa da kasa, ya buga wa Morocco wasanni 7 kuma ya zura kwallaye uku. Ya halarci gasar AFCON a shekarar 2002 a Mali, kuma ya zura kwallaye biyu a ragar Burkina Faso da ci 2-1.

Zerouali ya mutu a wani hatsarin mota a watan Disamba 2004, yana da shekaru 27.