Wasanni
Ɗan Najeriya Na Farko Da Ya Fara Buga Wasa A Gasar Premier League Ta Ingila
Efan Ekoku shi ne dan Najeriya na farko da ya fara buga gasar Premier ta Ingila.
Shi ne dan wasan Najeriya na uku a kan gaba wajen zura kwallaye a gasar Premier da kwallaye 52, bayan Kanu Nwankwo mai kwallaye (54) da Yakubu Aiyegbeni da ke da kwalleye (95).
A watan Satumban 1993, ya zama dan wasan Najeriya na farko da ya ci Hattrick a gasar Premier a karawar da Norwich City ta doke Everton da ci 5-1 a Goodison Park. A hakika ya zura kwallaye hudu a wasan.
A matakin kasa da kasa, ya buga wa tawagar kwallon kafar Najeriya wasanni shida.
Bayan da yayi ritaya, Ekoku yayi aiki a matsayin mai sharhi, kwararre da kuma manazarcin wasa.
An shigar da shi cikin Babban Birnin Norwich a cikin shekarar 2012.