Wasanni

Ɗan Kwallon Da juya Daga Mai Tsaron Raga Zuwa Ɗan Wasan Gaba

Mike Origi dan wasan kwallon kafar Kenya ne mai ritaya wanda ya fara taka leda a matsayin mai tsaron gida kafin ya koma dan wasan gaba.

Ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Kenya inda ya buga wasanni 48 kuma ya zura kwallaye 17.

Ya kuma taka leda a kungiyoyi kamar Shabana, Kenya Breweries, KV Oostende da Genk.

Dansa Divorck Origi yana taka leda a matsayin dan wasan gaba ga Liverpool da kuma tawagar kasar Belgium.