Wasanni
Ɗan Kwallon Da Ya Taɓa Zura Ƙwallaye 3 A Wasan Ƙarshe Ta Gasar Cin Kofin Duniya Ta Maza
Dan wasan gaba na Ingila Sir Geoffrey Hurst mai ritaya shi ne dan wasa daya tilo da ya zura kwallaye 3 a raga a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta maza.
Ya zura kwallaye uku a wasan da Ingila ta lallasa Jamus ta Yamma da ci 4-2 a filin wasa na Wembley a gasar cin kofin duniya a shekarar 1966.
Ko akwai wanda zai karya wannan tarihin?