Wasanni
Ƴar Wasa Ta Farko Da Ta Sanya Hijabi A Gasar Cin Kofin Duniya
Ƴar wasan baya ta kasar Morocco Nouhaila Benzina ta kafa tarihi inda ta zama ƴar wasa ta farko da ta fara saka hijabi a gasar cin kofin duniya.
‘Yar shekaru 25 ta sanya rigar Musulunci a lokacin da ta fara fitowa a gasar a wasan da kungiyar ta doke Koriya ta Kudu da ci 1-0.
Fifa ta ba da izinin sanya suturar kai saboda dalilai na addini a cikin 2014.
Morocco tana daya daga cikin kasashe takwas da suka fara buga gasar cin kofin duniya ta mata ta bana.
Benzina, wadda ke buga wasan kwallon kafa a kasar Morocco, ita ce ‘yar wasa ta farko da ta fara saka hijabi a gasar manyan kasashen duniya ta mata.
Ta kasance ‘yar canji da ba a yi amfani da ita ba a wasan farko da kasarta ta buga da Jamus, inda suka ci 6-0.