Ƴan Ƙwallon Afrika 7 Da Suka Mallaki Jiragen Sama Na Kan Su

Idan ana maganar ƴan wasan ƙwallon ƙafa mafiya arziki, yawancin suna tunanin manyan ƴan wasa ne kawai, wanda hakan ba haka yake ba. Don zama mai arziki yana buƙatar shiri. Waɗannan ‘yan wasan da muke gani ba lallai ba ne daga yanki ɗaya kuma don haka a cikin wannan labarin za mu ga ƴan kwallon Afrika 7 da suka mallaki jiragen kan su.

Ba tare da shakka ba, ’yan wasan ƙwallon ƙafa na wannan zamani suna da wadata ba tare da la’akari da gasar ko ƙasar da suke bugawa ba. Suna rayuwa mai cike da jin daɗi a lokacin hutu.

Samuel Eto Samuel

Eto’o dan kasar Kamaru ne amma ya fuskanci duk wata sana’ar kwallon kafa a kasashen waje. Eto’o ya taba buga wa kungiyoyin kwallon kafa da dama a Turai. Ya taba taka leda a Inter Milan, Real Madrid, Barcelona da Chelsea inda ya zura kwallaye sama da 200 a rayuwar shi.

Didier Drogba

Drogba ya kasance dan wasa mai kyau a lokacin da yayi fice kuma bajintar da yayi a Chelsea ya ba shi kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a lokuta biyu daban-daban; 2006 da 2009. Ya fito daga Ivory Coast.

Muhammad Salah

Muhammed Salah, dan wasan gaba na Masar da Liverpool na daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa na Afirka da ke karbar albashi mafi tsoka a duniya. Yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan da suka taimaka wa Liverpool ta daukaka gasar Premier bayan shekaru 30 na yunkurin.

A halin yanzu Salah yana samun misalin kwatankwacin dala miliyan $14 a matsayin albashin shekara-shekara a Liverpool.

Sauran ‘yan wasan kwallon kafar Afirka da ke da jiragen sama masu zaman kansu sun hada da kamar haka;-

Asamoan Gyan

Emannuel Adebayor

Pierre-Emeric Aubameyang

Suleiman Ali Muntari