Zargin Zamba: PDP Ta Nemi A Kori Minista Betta Edu, Da Kai Ta Kotu
Jam’iyyar PDP ta yi kira da a gaggauta korar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu, tare da gurfanar da ita a gaban kuliya bisa zargin wawure kudade biliyan N44 na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa, NSIPA, ciki har da miliyan N585.2 na rage fatara ga yan Najeriya.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana matsayin jam’iyyar a Abuja ranar Lahadi.
A cewarsa, zambar da ake zargin ta yi ne kawai na abin da ya kira “wawashe dukiyar kasa da ba a taba ganin irinsa ba, sata da kuma wawure dukiyar kasa da ake tafkawa a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda kusan ya kawo tattalin arzikin kasa ya durkushe”.
“Shin ba abin takaici da ban tausayi ba ne a ce wata minista da aka damka wa dukiyar al’umma don tallafa wa miliyoyin talakawan Najeriya da jam’iyyar APC ta talauta, ta juya ya karkatar da daruruwan miliyoyin Naira da aka ware domin jin dadin rayuwar talakawa?
“Ci gaba da zaman Betta Edu a matsayin minista yana da tsokana kuma ya kai ga satar mutane da kuma tursasa su yin mafi munin hakan.
“Hakan ya kara tabbatar da matsayin Jam’iyyar mu na cewa gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta ta daina cin hanci da rashawa; a yanzu mafaka ce ga barayi da masu wawure dukiyar kasa.
‘Yan Najeriya sun kadu matuka da rahotannin yadda Betta Edu da ko’odineta NSIPA ta dakatar, Halima Shehu da suka yi zargin yin sama-sama da wawure biliyoyin Naira yayin da ‘yan Najeriyar da ake nufi da wadannan kudade an bar su cikin wahala da matsu,” inji PDP. Kakakin ya kara da cewa.