Al'umma

Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya: Yabawa Masu Aikata Ba Dai-Dai Ba

Lokacin da aka yarda da ba dai-dai ba a matsayin dai-dai – Lokacin da za’a zo da dai-dan da ba za’a yarda da ita ba –  Daga Abdulwahab Said Ahmad.

Kamar kowa ya sani, a farkon watan wannan Agusta ne aka fara zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya wacce ta rikide ta koma ta’addanci a wasu sassan kasar da dama kamar Kano, Neja da sauran wasu jihohin kasar.

Wasu rahotanni sun bayyana an samu asarar rayuka da dukiyoyin gwamnati da na al’umma. Hakk kuma an yi ta arangama tsakanin bata gari da jami’an tsaro a yankunan ƙasar da dama.

– Abdulwahab Said Ahmad

Kowa ya sani abinda wannan yaron mai shekaru kasa da 16 yayi kuskure ne babba ta kowace fuska.

1. Kamar shi bai kamata ace ya fito zanga-zanga ba kan titi, kuma ya cire riga ya tari motar jami’an tsaro a gari irin na Maiduguri inda ake fama da barazanar tsaro wanda ake yin suicide bombing.

2. Idan da sun takashi ko harbi da cewa za ai aiken shi akai ba ruwan shi da masu zanga-zangar.

3. Babu wani mai hankali da zai so ace ɗan shi ko ƙanin shi ne yayi wannan aikin, domin yaron da zai tinkari mai bindiga gaba da gaba idan aka bata masa rai a gida sai kaji ana cewa anya kuwa uban shi ne ko uwar shi ce. Allah ya kiyaye.

4. Batun bashi gwarzon shekara da akace wani yayi har da alkawarin bashi kudi da daukar nauyin karatun shi wannan abin gwamnati ta duba ne, a ɗazu na ga yaran da suke jifan yan sanda sun zo wucewa bayan sun shige na kira daya daga ciki na tambaye shi dalilin yin jefar, sai yace nima gwarzon shekara nake son zama.

Ya kamata masu son taimakon al’umma su fi maida hankali wajen taimakon wadanda ya dace ba kokarin zaburar da yara da matasa ba wajen aikata ba dai-dai ba da sunan sun burge kuma su ringa karramasu.

Wannan abinda yaron nan yayi ba dai-dai bane kuma a gaya ragowar yara bada haka ake neman suna ba. Duk wannan matsalar ta lalacewar tarbiya da haka muka janyo ta.