Labarai

Zanga-Zanga Ta Barke A Abuja, Sun Nufi Majalisar Dokoki

Kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a halin yanzu suna gudanar da gagarumin zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja.

Zanga-zangar sama da 5,000 da suka kasance cikin lumana, sun fara haduwa ne a Unity Fountain, Abuja, kusa da otal din Transcorp Hilton, inda suka yi da ma’aikatar shari’a ta tarayya kafin su wuce zuwa majalisar dokokin kasar.

A majalisar dokokin kasar, da farko jami’an tsaro sun hana gungun masu zanga-zangar shiga harabar ginin, amma da manyan jami’an su suka shiga tsakani, sai aka bude kofar.

DAILY POST ta tuna cewa jam’iyyar Labour ta dage kan gudanar da zanga-zangar domin bayyana kokensu kan halin kuncin da akasarin ‘yan Najeriya ke ciki tun bayan da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin cire tallafin man fetur.

Dukkanin shugaban NLC, Joe Ajaero, da takwaransa na TUC, Festus Osifo, sun kasance a kan gaba wajen jagorantar zanga-zangar a babban birnin kasar.

Cikakkun bayanai daga baya.