Zagin Annabi Muhammad (SAW) Bai Zama Ƴancin Faɗin Albarkacin Baki Ba – Putin

Shugaba Viladmir Putin na Rasha

A yayin taron manema labarai na shekara-shekara, Putin ya bayyana mahimmancin yancin zane-zane ba tare da cikas ga yancin addini ba.

Putin ya ce bai kamata yancin zane-zane/fasaha ba ya keta wasu yanci ba.

Putin yace zagin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallama) ba zai zama hujjar yancin fadin albarkacin baki ba.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya ce zagin Annabi Muhammad ba ya a matsayin yancin fadin albarkacin baki.

Zagin annabi “cin zarafin yancin addini ne da kuma keta alfarmar mutane masu da’awar Musulunci,” in ji Putin a yayin taron manema labarai na shekara-shekara, in ji kamfanin dillancin labarai na REUTERS.

Putin ya kuma soki yadda ake yada hotunan yan Nazi a shafukan yanar gizo kamar wanda aka yi wa lakabi da Regiment na dawwama da aka sadaukar wa Rashawa da suka mutu a yakin duniya na biyu.

Putin yace wadannan ayyukan suna haifar da ramuwar gayya na masu tsattsauran ra’ayi, inda ya buga misali da harin da aka kai ofishin editan mujallar Charlie Hebdo dake birnin Paris bayan buga zane-zane na ma’aiki.

Yayin da yake yaba wa yancin yan zane gabaɗaya, Putin yace yana da iyaka kuma bai kamata ya keta wasu yanci ba.

Rasha ta samo asali ne a matsayin kasa mai yawan kabilu da masu yarda da juna, don haka Rasha, in ji shi, sun saba da mutunta al’adun juna.

A wasu kasashe, wannan girmamawa ta zo da karanci, in ji Putin.