Yan Najeriya Zasu Shiga Duhu, Yayin Da Tashar Raba Wuta Ta Sake Lalacewa

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu Plc, EEDC, a ranar Litinin ya sanar da kwastomominsa kan lalacewaar tashar wutar, wanda ya haifar da katsewar wutar a duk yankin Kudu maso Gabas.

Hukumar ta EEDC a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban sashen sadarwa na kamfanin Emeka Eze, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin.

Sai dai kamfanin ya tabbatar wa mazauna yankin cewa ana kokarin ganin an dawo da wutar nan ba da dadewa ba.

Sanarwar ta ce, “Hakan ya haifar da rashin wadatar wutar ga dukkan tashoshin mu na TCN. Saboda haka, ba mu iya ba da wuta ga abokan cinikin mu a jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, da Imo.

“Duk da haka, a hankali ana shawo kan lamarin yayin da muka samu wutar a tashar Awada TCN, Onitsha, da karfe 7:30 na safe.

“Muna ci gaba da sadarwa tare da hukumomin da abin ya shafa muna jiran cikakken maido da wutar daga Cibiyar Kula da Wuta ta Kasa, NCC, Oshogbo.”