‘Yan Arewa Na Ƙorafi Akan BBC Hausa
‘Yan Arewa suna korafi akan cewa BBC Hausa ta kasa yin magana akan halin da al-ummar yankin suke ciki, musamman a cikin wa ‘yan nan kwanakin da ake ta nuna jimami kan halin da yankin Arewa yake ciki.
Zancen gaskiya BBC Hausa basu kyauta mana ba mu ‘yan Arewa, dalilina kuwa shine duk Najeriya babu wata jaridar da ‘yan Arewa suke following kuma suka bata yadda sama da shafin BBC Hausa.
Kusan kaso 50 na ‘yan Arewa suna following din shafin jaridar a Facebook, Twitter. A irin wannan yanayin da ‘yan Arewa suka kauracewa murnar samun ‘yan cin kai, suka fito kafofin sada zumunta suna ta nuna alhinin su kan halin da ‘yan kasar suke ciki, ya kamata shafin BBC Hausa ya yi mana kara, ya nunawa Duniya halin da muke ciki.
Duk wani Dan Arewa da yake son sakon shi ya isa ga mahukuntar kasar da Duniya tasan halin da yake ciki, yafi gamsuwa yaga sakonshi a shafin BBC Hausa, domin yasan duk wani babba a kasar yana following din su, koda baijin Hausa yana danna Translation zuwa turanci domin ya fahimci abunda aka rubuta.
Muna kira ga ma’aikatan gudanarwa na BBC Hausa da su gyara irin wannan matsalar, domin idan har basu gyara ba, suka fusata ‘yan Arewa na tabbata mutanan Arewa zasu iya yiwa shafin bore tare da kaurace mishi kamar yadda suka yiwa wata jarida a shekarun baya.
Kuma na tabbata idan suka yiwa shafin BBC Hausa irin haka, duk karfin shafin sai ya girgiza, domin fiye da kaso 50 masu following din shafin duk ‘yan Arewa ne.
Sannan mu ‘yan Arewa ya kamata mu sani, shafin BBC Hausa bana Dan Arewa bane, bana dan Najeriya ko Afrika bane. Tun tuni an riga da anyi mana babbar illa wurin rashin manyan jairdu a yankin namu, kuma hakan yana da alaka da laifin manyan mu na Arewa.
Amma Insha Allahu a matsayinmu na matasa masu tasowa a harkar yada labarai, muna shiri irin namu na ganin mun samar da irin wa ‘yan nan manyan jairdun, amma dole muna bukatan Support daga kowane bangare wanda ya shafi kayan aiki, da sauran su. Muna ji a ranmu Insha Allahu burinmu zai cika.
Daga: Comr Abba Sani Pantami