Wani Mutum Ya Kashe Matar Shi Mai Yara 5 Akan Biredi

Wata mata mai suna Ogochukwu Anene, wacce aka fi sani da Ada Akwa, ta rasu bayan da mijin ta, Ndubuisi Wilson Uwadiegwu ya yi mata duka a Awka, jihar Anambra.

An tattaro cewa marigayiyar, Ogochukwu, ya auri wanda ake zargin ya kashe, Ndubuisi. Auren nasu ya sha fama da tashin hankalin gida da dama. Rahotanni sun ce ma’auratan suna da ‘ya’ya 5 da suka kunshi maza 4 da mace daya.

Dan su na farko wanda yaro ne dan shekara 14 ne ya bada labarin yadda lamarin ya faru. Ya ce Ndubuisi ya yi amfani da madubi a matsayin kayan aiki wajen dukan matar shi.

Ya bayyana cewa marigayiyar ta nemi wanda ake zargin ya ba su kudi domin ta samo musu biredi da za su ci.

An samu rashin jituwa da ita yayin da wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ba shi da kudi tare da shi. Nan ta wuce ta siyo biredi da kudin ta kawai mijin ta yaje kicin ya gama biredin duka.

Hakan ya fusata, Ogochukwu ta ci gaba da fuskantar mijin ta, tana tambayar shi dalilin da ya sa zai cinye biredin ba tare da ya rage wa yaran ba.

Mijin ta ya fusata da tambayoyin kuma, sakamakon haka, ya sanya mata firgici. Ya lakada mata duka yana dukanta wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar ta.

Rahotanni sun bayyana cewa mijin ya dade yana shirin binne matar ba tare da amincewar surikin shi ba. Hakan dai ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.