Yadda Jirgin Kasa Ya Darkake Wata Mota Da Mutanen Da Ke Ciki A Abuja

Kwanaki kadan bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna, an samu wani hadari.

Arewa Times ta tattaro cewa motar wacce wata mata ke tuki da har yanzu ba a tantance ba jirgin ya murkushe motar a unguwar Kubwa a Abuja ranar Alhamis.

Bidiyon hadarin ya nuna cewa jirgin ya murkushe wata bakar mota kirar Toyota Camry daga bangaren direban yayin da motar ke tsallaka titin jirgin.

Kazalika kakakin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Mahmood Yakoob, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya kasa bayar da cikakken bayani har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Har ila yau, ba a iya tabbatar da yanayin direban motar ba tukuna.