Labarai
Wasu Matasa Sun Sace Faston Cocin Su, Asiri Ya Tonu
Ana cewa wasu matasa sun yi garkuwa da wani babban fasto a garin Panshin dake jihar Filato, har ma kuma suka nema abiya kudin fansa naira miliyan ashirin da biyar (N25 miliyan).
Kafin matasan su kai ga karban kudin fansar, sun yi rashin sa’a sun shiga hannu cikin ikon Allah.
An bayyana cewa dukkan matasan masu halartar wannan cocin faston ne.
Jihar Filato ta sha fama da haren-haren ta’addanci da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, kuma a mafi yawancin lokuta ana dora alhakin wannan ta’addanci akan Fulani makiya ne.