Yaro Mai Shekaru 18 Ya Kashe Matar Aure A Kano Daga Satar Waya

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Abdussamad Suleman bisa zargin kashe wata matar aure mai suna Ruqayya Jamilu bayan ya shiga gidan ta domin satar waya.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, an kama yaron ne biyo bayan wani korafi da mijin marigayiyar ya kai ofishin yan sanda na Dorayi.

Bincike ya nuna cewa Abdussamad da daya daga cikin abokan shi, Muazzam Lawan sun shiga gidan matar ne domin su saci kaya masu daraja, amma nan take Ruqayya ta gane wanda ake zargin sannan ta fara ihun neman agaji.

Abdussamad ya yi amfani da wata karamar katako inda ya buge ta sau da yawa a kai wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince cewa ya kashe Ruqayya ne bayan ya gano cewa ta gane shi kuma hakan na iya haifar masa da matsala.

“Ta gane ni a lokacin da nake satar wayoyin, na yi amfani da wata katako da aka yi na buga mata a kai sau da yawa, sannan na bugi ya’yan ta guda biyu.” Wanda ake zargin ya bayyana.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da ya’yan ta biyu ke samun kulawa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.