Wani Yaro Ɗan Shekara 17 Ya Kashe Kansa A Bauchi

Wani yaro dan shekara 17 mai suna Betwom Bitrus ya kashe kansa a karamar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a daren Laraba a Bauchi.

Ya ce marigayin ya je wani rafi da ke yankin domin yin wanka amma bai koma gida ba.

Kakakin ya ce: “Mun samu rahoto daga wani mutum cewa ɗan’uwansa, Betwom Timothy mai shekara 17, ya bar gida fon yin yayi wanka a rafi a ranar 12 ga Satumba amma bai koma gida ba.

“Don haka ‘yan uwa suka gudanar da bincike a kansa inda a karshe suka gano gawarsa a rataye a jikin bishiya da soso da kuma najasa a kan wando a wani daji da ke kusa da garin Bogoro.

“Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Auwal Muhammad, ya umarci DPO da jami’an tsaro da su je wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe gawar zuwa babban asibitin garin Bogoro inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa da isowa.

“An ba da gawarsa ga iyalin don binne shi.”