Wani Mutum Zai Mutu Ta Hanyar Rataya Bisa Laifin Fille Kan Wata Mata A Jigawa

Babbar Kotun Jihar Jigawa da ke Birnin Kudu ta yanke wa Isyaku Wakili Gwanto hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe Malama Malora Adamu.

Tun da farko dai an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa zargin fille kan wanda aka kashe da adda a matsugunin Fulani Duliyari da ke karamar hukumar Kirikasamma.

Alkalin kotun, Mai shari’a Musa Ubale ya ce laifin kisan kai ne da hukuncin kisa a karkashin sashe na 221 (b) na kundin laifuffuka.

Mai shari’a Ubale ya ce lauyan mai shigar da kara ya tabbatar da karar sa ba tare da wata shakka ba, don haka ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya domin ya zama tirjiya ga wasu.