Wani Mutum Ya Kashe Ɗan Aiken Kotun Da Ya Kai Masa Sammaci

Wani mutum a jihar Adamawa mai suna Linus Dimas ya kashe ma’aikacin kotu da aka aika masa domin ya kai masa sammaci.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a yammacin ranar Talata, inda ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargin a ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, a lokacin da ake zargin ya kashe ma’aikacin da ya je kai masa sammacin kotu.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Suleiman Nguroje, ta ce Linus Dimas mai shekaru 43, mazaunin Kugama Wuro Jibir ne a karamar hukumar Mayo Belwa.

A cewar sanarwar: “Wanda ake zargin, a ranar 18 ga watan Disamba, 2023, ya ki amincewa da sammacin kotu da Yauba Usman, ma’aikacin kotun yankin Nasarawo Jereng ya kai masa, tare da daba masa wuka sau da dama, wanda hakan yayi masa rauni sosai.”

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, nan take aka garzaya da magatakardar kotun zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.