Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Har Lahira Wajen Gwajin Maganin Bindiga

Wani dan Najeriya mai suna Yusuf Adamu ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata bayan ɗan shi ya harbe shi a lokacin da yake gwada maganin bindiga a jihar Adamawa, kamar yadda Sahara Reporters ta samu.

Rahotanni sun bayyana cewa Adamu ya umarci dan gidan na shi, Suugbomsumen Adamu da ya harbe shi domin a gwada ingancin wasu sabbin ganyen da aka samu da nufin maganin harbin bindiga.

An tattaro cewa marigayin yayi takama da cewa sabbin layukan da aka samu suna kare shi daga harbin bindiga; don haka umarnin da ya ba dan shi ya harbe shi.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata a kauyen Sankipo da ke karamar hukumar Jada.

A cewar ‘yan sandan, har yanzu wanda yayi harbin yana hannun su.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje yace, “ana tsare da wanda yayi harbin.

‘’Yan sanda za su yi bincike sosai kan lamarin tare da tabbatar da an yi adalci, ba tare da la’akari da alakar mamacin da wanda ake zargin yayi harbin ba.