Labarai

Wani Matashi Ya Kashe Kan Shi Akan Bashin ₦250,000

Mutuwar Saifullahi Salisu dan shekara 30 dan garin Shata, Maikunkele a karamar hukumar Bosso ta jihar Neja, wanda ake zargin ya rataye kansa, ya jefa mazauna yankin cikin firgici da rudani.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya kashe kansa ne biyo bayan rashin biyan bashin naira ₦250,000 da mutane ke bin shi.

DAILY POST ta samu labarin faruwar lamarin a safiyar ranar Litinin.

Wasu mazauna garin Shata sun shaidawa DAILY POST cewa makwabtan sa ne suka gano gawar Salisu a rataye da igiya a cikin dakin kwanansa a ranar Litinin.

A cewarsu, an binne gawarsa. An bayyana shi a matsayin matashi mai aiki tuƙuru da dama.

Budurwar tasa mai suna Rebecca Musa, ta bayyana cewa marigayin ya sanar da ita ne, lokacin da ta lura ya damu cewa wasu mutanen yankin na bin shi kudi naira ₦250,000.

A cewarta: “Ya gaya min cewa wadanda yake bin shi bashi sun fara neman kudinsu, kuma ya kasa biya. Ya gaya mani cewa al’amarin ya dame shi, kuma bai san yadda zai warware basussukan ba. Ban san hakan zai haifar masa da kashe kansa a kai ba.”

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce an dauke gawar aka kai dakin gawarwaki na babban asibitin kafin a sako gawar ga iyalan.

Ya kuma kara tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.