Wane Ne Saleh Al-Arouri? Shugaban Hamas Da Isra’ila Ta Kashe A Lebanon

Saleh Al-Arouri shi ne mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Falasɗinawa ta Hamas, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa reshen kungiyar Falasdinu masu dauke da makamai (Hamas), wato Qassam Brigades.

An haifi Al-Arouri a garin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye a shekarar 1966.

Ya dade yana zaman gudun hijira a Lebanon bayan ya shafe sama da shekaru 15 a gidan yari na Isra’ila.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, Al-Arouri ya kasance mai magana da yawun Hamas da dabarunta a yakin Gaza.

A watan Disamba na shekarar 2023, Al-Arouri ya shaidawa Al Jazeera cewa Hamas ba za ta tattauna batun musayar fursunoni ba kafin kawo karshen hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza.

“Zamu yi turjiya da juriya, domin wannan shine tsarin dukkan mayakan mu,” in ji shi. “Babu tsoro ko ja da baya. Zamu yi nasara.”

A watan Oktoba na 2023 ne sojojin Isra’ila suka rusa gidansa da ke kusa da Ramallah.

An kashe Al-Arouri da sauran shugabannin Hamas da mabiyan ta a wani harin da Isra’ila ta kai a kasar Lebanon da jirgi marar matuki a ranar 2 ga watan Janairun 2024.

Gwamnatin Amurka ta ayyana shi a matsayin “dan ta’adda na duniya” a cikin 2015 kuma ta fitar da tukuicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya ba da bayanai a kai.