Labarai

UTME 2023: Dalibar Da Ta Samu Maki 362 Sakamakon Bogi Ne – JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta yi ikirarin cewa wata daliba mai suna Ejikeme Mmesoma ta kara makin sakamakonta tare da bayyana kanta a matsayin wadda ta fi samun maki a jarrabawar gama gari ta 2023.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da hukumar ta JAMB ta fitar ranar Lahadi.

An ce Ejikeme ta samu tallafin karatu ne daga kamfanin Innoson Motors a dalilin haka, kuma da gwamnatin jihar Anambra ta karrama ta kafin fallasa ta.

“Babban abin tausayi a cikin su duka shi ne batun Miss Ejikeme Joy Mmesoma, wacce ta yi ikirarin cewa ta samu maki 362 a 2023 UTME kuma Cif (Dr.) Innocent Chukwuma ya ba ta kyautar N3m.

“Hatta gwamnatin jihar Anambra ta shirya karrama ta a lokacin da daya daga cikin jami’anta ya kira hukumar JAMB domin tabbatar da ikirarinta, sai dai hukumar ta bayyana cewa Miss Ejikeme Joy Mmesoma ta samu maki 249 ba 362 ba. da’awar. Ta yi amfani da sakamakonta na UTME ne don yaudarar jama’a da zamba don samun guraben karatu da sauran su,” in ji sanarwar a wani bangare.

Hukumar JAMB ta kuma ce ta gano wani dan dalibi da yayi damfara da yayi ikirarin cewa ya samu jimillar maki 380 a jarabawar UTME da ta gabata.