Al'umma

Tun Bayan Musulunta Ta Ba Wanda Ya Neme Ni Da Aure Sai Zina – Muneerat Abdulsalam

A cewar shahararriyar mai janyo cece-cuce a shafukan intanet, Muneerat Abdulsalam, tun bayan musuluntar ta nake fuskantar manyan matsaloli a cikin rayuwarta, inda tace tuni Iyayen suka sallama ta.

A cewarta; “Musulmi da nake cikin su ba su nuna mini soyayyar da ta kamata ba, masu kuɗi sun mayar da ni wata hanya ta kashe ƙwaɗayi kawai”.

Waɗannan sune kalaman Muneerat kenan a wani faifan bidiyo da ta fitar tana hawaye, inda take bayyana irin halin ƙuncin rayuwa da ta shiga, dalilin da ya sanya har ta yi izgilancin da tayi na iƙirarin ficewa daga addinin Musulunci a baya.

“Wasu ne suka fusata ni, suna yi min gorin Musulunci, suna kira na da Yare, shi yasa na ce na bar addinin Musuluncin in dole ne! Amma har yanzu ni Musulma ce, kuma ina fatan mutuwa a cikin addinin Musulunci”. Inji ta

Muneerat ta kara da cewa “saboda soyayyata da addinin Musulunci na yi hannun riga da mahaifina domin shi ba musulmi ba ne, na guji ‘yan uwana na jini na dawo cikin Hausawa Musulmai.

Sannan kuma tunda na musulunta babu wanda ya ja ni a jiki, sai kyama ta da gori da ake yi min kowane lokaci, kuma duk manyan da suke bibiyata babu wanda yake nema na da aure sai dai su nemi na zo su yi zina da ni su biya ni”.