Labarai

Tsohuwa Mai Shekaru 70 Ta Haifi Ɗanta Na Farko A Duniya

Wata mata da ake kyautata zaton tana da shekaru kusan 70 a duniya, ta samu nasarar haihuwar danta na farko ta hanyar “mu’ujiza” ta IVF a yammacin Indiya.

Dokta Naresh Bhanushali, likitan mata daga garin Bhuj na jihar Gujarat, ya shaida wa jaridar The Independent cewa yayi nasarar gudanar da aikin a kan Jivuben Vallabhai Rabari kuma ta haifi danta a ranar 9 ga Satumba.

“Wannan lamari ne da ba kasafai ba, za ku iya kiransa abin al’ajabi.  Na yi shekaru 20 ina aiki kuma na gudanar da aiki na IVF sama da 1,000 amma ban taɓa ganin irin wannan ba. Duk da yake muna farin ciki cewa aikin ya yi nasara, har yanzu muna kira ga mutane da kada su yi ƙoƙarin yin ciki a lokacin tsufa,” in ji Dr Bhanushali.

Bayanan shigar asibiti, wanda jaridar The Independent ta gani, ba ta lissafo ranar da aka haifi Ms Rabari ba saboda ba ta da wasu takardu da za su tabbatar da shekarunta kamar katin zabe ko takardar shaidar haihuwa – lamarin da ya zama ruwan dare a yankunan karkarar Indiya.  Sai dai likitocin sun ce shekarunta sun kai 70.

Wani manomi daga kauyen Rapar da ke da nisan kilomita 100 daga Bhuj, Ms Rabari ya bukaci likitocin da su duba fiye da shekarunta su gwada aikin da take so saboda tana da burin samun haihuwa.