Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno, Shuwa Ya Rasu Ƴan Kwanaki Bayan Ya Bar Ofis

Tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Usman Jidda Shuwa, ya rasu.

Shuwa, wanda yayi aiki a karkashin Gwamna Babagana Umara Zulum har zuwa ranar 28 ga Mayu, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Majiyoyin iyalan da suka zanta da Daily Trust sun tabbatar da cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Shuwa, an haife shi a shekara ta 1958, ƙwararren mai gudanar da mulki ne wanda ke da tarihin aiki a matakin jiha da tarayya.