Tsawa Da Walƙiya Sun Kashe Mutane 18 Da Dabbobi 40 A Indiya
Akalla mutane 18 ne suka mutusakamakon tsawa da aka yi a yammacin jihar Gujarat a kasar Indiya yayin da aka yi wata mummunar guguwar hadari a ranar Lahadin da ta gabata, in ji jami’ai.
Ba a sa ran irin wannan babban guguwar ruwan sama a Gujarat a cikin watannin hunturu ba, kuma ruwan sama mai tsanani ya shafi mutane da yawa.
Yayin da ambaliyar ruwa da walƙiya ke kashe mutane da yawa a Indiya a kowace shekara, masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa hauhawar yanayin zafi a duniya na haifar da bala’in yanayi mai tsanani.
Akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda akalla 18 daga cikinsu suka mutu sakamakon tsawa, kamar yadda hukumomin jihar Gujarat suka bayyana a cikin wata sanarwa da yammacin jiya Lahadi.
An kuma sanar da cewa akalla dabbobi 40 sun mutu q lamarin.
Ministan cikin gida Amit Shah ya ce ya yi matukar bakin ciki da mutuwar, a cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X.
Source: ABS-CBN News