Tinubu Ya Dakatar ministar Jinkai, Betta Edu Kan Zambar Miliyan N585
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr. Betta Edu daga aiki ba tare da bata lokaci ba.
Idan dai za a iya tunawa, fadar shugaban kasa ta ce hukumomin da suka dace na gudanar da bincike kan zambar kudaden da Ministar ta karkatar na naira miliyan N585.189.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce za a dauki matakin da ya dace bayan bincike.
Jaridar Arewa Times Hausa ta rawaito cewa an karkatar da kimanin Naira miliyan N585.189 na marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun, da Legas zuwa wani asusun banki na sirri.
Wannan ya haifar da tashin tarzoma da kuma kiran sauke Edu da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.
A cikin wata takarda da Edu ta sanya wa hannu kuma ta mika wa ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Ministan ta bada umarnin a fitar da Naira miliyan N585.189 a cikin wani asusun sirri daya na Bridget Mojisola Oniyelu.
Takardar da aka bankado ta bayyana cewa an biya kudin a asusun Oniyelu.
A cikin wannan bacin rai, Edu, a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata na musamman kan harkokin yada labarai, Rasheed Zubair ya fitar, ta ce biyan kudin ya biyo bayan tsarin da ya dace.