Tarihi

Tarihin Rayuwar Hajjaj Bin Yusuf Da Mutanen Ya Kashe A Mulkin Shi

Al-Hajjaj bin Yusuf al-Thaqafi ya kasance fitaccen mutum ne kuma mai yawan cece-kuce a tarihin Musulunci na farko, wanda aka san shi da matsayinsa na gwamnan Iraki a karkashin Khalifancin daular Bani Umayyawa a karshen karni na 7.

An haifi Hajjaj a shekara ta 661 miladiyya, tun farko soja ne kuma dan siyasa, ya yi fice saboda biyayyarsa ga daular Umayyawa. A lokuta da dama ana tunawa da Hajjaj bisa irin kwazonsa na gudanar da mulki da irin gudunmawar da ya bayar wajen samar da ababen more rayuwa a yankin da suka hada da gina tituna da na ban ruwa.

Amma kuma sunansa ya lalace saboda mugunyar dabi’ar danne masu adawa da suka da ya yi, musamman a zamanin da ake fama da tashin hankali da ya biyo bayan tarzoma da tawaye na Musulunci.

Mulkin Hajjaj ya kasance yana da kaushi da rashin tausayi ga wanzar da doka. Murkushe tashe-tashen hankula daban-daban, musamman tawayen da Abdullah ibn Al-Zubair ya jagoranta, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, har da Al-Zubair da kuma fargaba a tsakanin masu adawa da shi.

Kiyasin adadin mutanen da Hajjaj ya kashe a lokacin mulkinsa ya sha banban. Wasu sun ƙiyasta cewa ya kashe mutane sama da 120,000 zuwa 125,000 na daga Sahabbai da dai-daikun mutane. Amma ana kyautata zaton an kashe dubban mutane ne kai tsaye ko kuma suka mutu sakamakon manufofinsa na zalunci da kuma yakin neman ci gaba da zama kan mulki.

Gadon da Hajjaj ya bari kuwa abu ne mai sarkakiya; yayin da ake ganinsa da karfafa daular Banu Umayya da fadada yankunanta, zaluncin hanyoyinsa ya sa aka bayyana shi a matsayin azzalumi a tarihin Musulunci.

Bugu da kari, duk da tsananin mulkin da Hajjaj ya yi, tasirin da Hajjaj ke da shi kan ci gaban daular Musulunci ta farko na da matukar muhimmanci, wanda ke nuni da irin kalubalen da ke tattare da gudanar da mulki a lokacin da ake fama da rigingimun siyasa.