Sojojin Burkina Faso Sun Ce Yunkurin Juyin Mulki Ya Ci Tura, An Kama Masu Yunkurin

Hukumomin leken asiri da jami’an tsaron kasar sun dakile yunkurin juyin mulkin da aka so yiwa shugabannin sojin Burkina Faso.

Shugabannin sojojin Burkina Faso sun fada a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, wasu hafsoshin soji da sauran su sun shirya kwace mulki tare da jefa kasar cikin “rikici”.

“An kama jami’ai da wasu da ake zargi da hannu a wannan yunkurin na tada zaune tsaye, wasu kuma ana nemansu sosai,” in ji kakakin rundunar sojin kasar Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo a wata sanarwa da ya fitar ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

An yi yunkurin juyin mulkin na baya-bayan nan a ranar Talata, a cewar sanarwar.

Gwamnatin sojan ta ce za ta nemi yin “dukkanin haske kan wannan makirci” kuma ta yi nadamar cewa “jami’an da rantsuwar kare kasarsu ta haihuwa sun shiga wani hali na wannan dabi’a”.

Daga baya mai gabatar da kara na sojin kasar ya ce an kama mutane hudu kuma biyu suna kan gudu. An bude bincike ne bisa “sahihan zarge-zarge game da wani shiri da aka yi wa jami’an tsaron jihar”, in ji mai gabatar da kara.