Labarai

Sojojin Burkina Faso Da Ƴan Sa-Kai 53 Sun Mutu A Arangama Da Ƴan Tawaye

Akalla jami’an tsaron Burkina Faso 53 ne aka kashe a wani kazamin artabu da mayakan ‘yan tawaye a arewacin kasar, a cewar rundunar.

Sojoji 17 da masu aikin sa kai 36 ne suka mutu a wani hari da aka kai a gundumar Koumbri da ke lardin Yatenga a ranar Litinin, in ji sanarwar a ranar Talata.

Sanarwar ta kara da cewa, an baza jami’an tsaro a garin domin samun damar sake tsugunar da mazauna yankin da mayakan suka fatattake su sama da shekaru biyu da suka gabata.

“Wannan aikin na matsananciyar tsoro ba za a hukunta shi ba. Ana ci gaba da kokarin murkushe sauran ‘yan ta’addan da suke gudu,” in ji sanarwar, ta kuma kara da cewa an kashe da dama daga cikin mayakan tare da lalata kayayyakin yakinsu.

Rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin