Sojoji 36 Da Aka Kashe A Neja – Inji Hedkwatar Tsaro
Hedikwatar tsaro ta DHQ ta bayyana cewa an kashe jami’anta 36 a jihar Neja.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da take bayar da cikakken bayani game da asarar rayuka a harin kwantan bauna da sojoji suka yi a jihar Neja da wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi hadari a ranar 14 ga watan Agustan 2023.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin taron manema labarai na makwanni biyu.
Da aka tambaye shi musabbabin hatsarin jirgin mai saukar ungulu Buba, ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin, ya kuma bukaci ‘yan kasar da su yi hattara da farfagandar ‘yan ta’adda, su kuma kasance masu kishin kasa.
‘Yan tada kayar bayan sun yi wa sojoji kwanton bauna a yankin Zungeru da ke jihar, kuma wasu jiga-jigan sojojin na sojojin Najeriya sun biya kudin sabulu.
Hakazalika, jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-171 na rundunar sojojin saman Najeriya da ke aikin kwashe mutanen da suka jikkata ya yi hatsari a ranar Litinin a karamar hukumar Shiroro da ke jihar.