Labarai
Shugaban Kasar Zambabwe, Mnangagwa Ya Lashe Zaɓen Wa’adi Na Biyu
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya lashe wa’adi na biyu kuma na karshe a sakamakon da ‘yan adawa suka yi watsi da shi tare da yin tambayoyi da masu sa ido.
Mnangagwa wanda ya karbi ragamar mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Robert Mugabe bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2017, ana kyautata zaton zai sake tsayawa takara duk da matsalar tattalin arzikin da kasar ke ci gaba da fama da shi, inda masu sharhi suka ce fafatawar ta yi kaca-kaca da jam’iyyar ZANU-PF, wadda ita ce ta lashe zaben. ya mulki kasar tun bayan samun ‘yancin kai da kawo karshen mulkin ‘yan tsiraru farar fata a shekarar 1980.