Labarai

Shugaban Kasar Iran, Ibrahim Raisi Yayi Hatsarin A Jirgin Helikwafta

Wani jirgin sama mai saukar ungulu, helikwafta dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ministan harkokin wajen kasar da kuma wasu jami’ai ya fadi a yankin arewa maso yammacin kasar Iran a ranar Lahadi, lamarin da ya haifar da gagarumin aikin ceto a wani dajin da ke cike da hazo yayin da aka bukaci jama’a da su yi addu’a.

Mai yiwuwa hatsarin ya zo ne a daidai lokacin da Iran karkashin jagorancin Raisi da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ali Khamenei suka kaddamar da hari da makami masu linzami da ba a taba ganin irinsa ba a kan Isra’ila a watan da ya gabata tare da inganta sinadarin Uranium kusa da matakin makaman.

Har ila yau Iran ta fuskanci zanga-zangar adawa da tsarin mulkinta na Shi’a na tsawon shekaru da dama kan tattalin arzikinta da kuma ‘yancin mata – abin da ya sanya lokacin da ya fi mayar da hankali ga Tehran da makomar kasar yayin da yakin Isra’ila da Hamas ke ruruwa a Gabas ta Tsakiya.

Raisi yana tafiya ne a lardin Azabaijan ta Gabashin Iran. Gidan talabijin na kasar ya ce abin da ya kira “sauka mai wuya” ya faru a kusa da Jolfa, wani birni da ke kan iyaka da kasar Azarbaijan, mai tazarar kilomita 600 (mil 375) arewa maso yammacin Tehran babban birnin kasar Iran. Daga baya, gidan talabijin na gwamnati ya sanya shi a gabas kusa da ƙauyen Uzi, amma bayanai sun ci gaba da cin karo da juna har ya zuwa haɗa wannan rahoto.