Shugaban Kasar Gambia, Adama Barrow Ya Hana Kan Shi Da Jami’an Gwamnati Tafiya Kasashen Waje

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow, ya haramtawa duk wani tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da jami’ai da suka hada da shi, domin rage kudaden da jama’a ke kashewa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ebrima Sankareh, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Asabar a Banjul, ya ce shugaban ya sanya hannu kan wata doka ta “dakatar da duk wata tafiye-tafiye zuwa ketare na sauran shekara.

A cewarsa, shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, ministocin gwamnati, manyan jami’an gwamnati, ma’aikatan gwamnati, da ma’aikata a dukkanin cibiyoyi da hukumomin gwamnati an hana su fita tafiye-tafiyen kasashen waje bisa tsarin zartarwa.

Sai dai ya kara da cewa tarurrukan da shigar Gambia ya zama tilas kuma tafiye-tafiyen kasashen waje gaba daya da aka samu daga majiyoyin waje ba zai shafi wannan odar ba.