Shugaban Ƙungiyar Wagner Ta Rasha Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

Shugaban rukunin Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama.

Jirgin mai zaman kansa ya yi hatsari inda mutane kusan 10 da ke cikinsa suka mutu.

Rahotanni sun ce wasu da ake zargin sojojin Rasha ne suka harbo jirgin mai zaman kansa a yankin Tver da ke arewacin birnin Moscow.

Kwanan nan, Prigozhin ya yi yunkurin juyin mulki a kan Putin.

Prigozhin ya jagoranci wani boren da bai yi nasara ba kan sojojin Rasha a watan Yuni.

Putin ya bayyana Prigozhin a matsayin “maci amana”.