Labarai

Shahararren Malamin Addinin Musulunci, Gero Argungu Ya Rasu

Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu.

Sakataren kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a wa Iqamatus Sunnah, (JIBWIS), Kabir Muhammad Haruna ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa, malamin ya rasu ne a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, bayan gajeruwar rashin lafiya.

“Mu daga Allah muke, kuma zuwa gare Shi muke komawa.

“Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu.

“Za a yi jana’izar marigayin gobe Alhamis kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Za a sanar da lokacin jana’izar nan gaba kadan,” in ji Sakataren JIBWIS na kasa