Labarai

Serie A: Napoli Zata Sake Tattauna Wani Sabon Kwantiragi Da Osimhen

Daraktan wasanni na Napoli, Mauro Meluso ya bayyana cewa kungiyar za ta sake tattaunawa da Victor Osimhen nan da ‘yan makonni masu zuwa.

Osimhen ya yi nisa da amincewa da sabon kwantiragi da zakarun Serie A bayan ya fusata da bidiyon TikTok da kulob din ya buga.

Ita ma Napoli ba ta ji dadi ba bayan da dan Najeriyar ya dawo daga buga wasan kasa da kasa da rauni a makon jiya.

Meluso, ya bayyana cewa Partenopei na shirin wani sabon zagaye na tattaunawa da wakilan dan wasan mai shekaru 24 a cikin makonni biyu masu zuwa.

“Za a yi wata ganawa tsakanin shugaban kasa da tawagar Osimhen cikin ‘yan makonni masu zuwa. Yana daga cikin wasan kuma ana buƙatar ɗan lokaci kaɗan don tunani game da shi, ” Calciomercato.com ya nakalto Meluso.

Dan wasan na Najeriya dai yana da kasa da shekaru biyu a kwantiraginsa da Napoli.