Sarkin Daura Mai Shekaru 90, Ya Auri Sabuwar Amarya Ƴar Shekara 20

Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya auri wata amarya ‘yar shekara 20, mai suna Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.

An haife shi a shekara ta 1931, an daura auren na shi a karamar hukumar Katsina tare da budurwar mai shekara 20 a wani ɗan karamin biki da aka gudanar.

An bayyana cewa sarkin ya biya kudin sadakin naira miliyan daya ga amaryar wacce diyar Fagacin Katsina ce, Iro Maikano.

Majiyoyi sun ce Sarkin ya auri mata fiye da daya matasa aƙalla hudu a cikin shekaru shida da suka wuce.

Wani dan karamin faifan bidiyo ya nuna yadda Magajin Garin Daura, Musa Umar, ya wakilci sarki a wajen daurin auren Fatiha.

Daily Nigerian