Al'umma

Sabuwar Alawar “Chocolate” Mai Giya A Ciki: Ayi Hattara

Yanzu wata abokiyar aikin aboki na ta ba shi chocolates (Alawa) da yawa kuma kala-kala, amma dai sai ta faɗa masa gaskiya cewa wannan ba irin tashi ba ce domin tana da giya a ciki.

Koda abokin nanws nayi Googling a intanet sai ya gano chocolate din tana da giya a cikin shi kuma har 14%, (ma’ana) mayen zai saka mutum yafi na wasu giyoyi da dama.

Misali: ita wannan chocolate din tafi Star Radler maye nesa ba kusa ba, domin Star Radler 2% na giya ne kawai a cikinta, ita kuma wannan chocolate din har 14% take da.

A taƙaicen labari, ba kowace giya ce alcohol percentage dinta yake iya kaiwa 14% ba. Duk da cewa na san chocolates masu giya gwargwado, amma dai gaskiya ban sanda wannan ba sai yanzu.

Gargadi

Gargaɗi ga ƴan uwa musulmai: ire-iren wadannan chocolates suna da yawa a kasuwa. Kafin ka saye wa yaran ka ko iyalin ka sai kayi kokari ka duba content din ciki, ko kuma purpose din don a halin yanzu harda chocolates din other rooms akwai.