Labarai

Rundunar Sojoji Ta Kashe Yan Bindiga 974, Ta Kwato AK-47 640 A Wata Ɗaya

Hedikwatar tsaro (DHQ) a ranar Alhamis ta ce sojojin da aka tura yankuna daban-daban na ayyuka a fadin kasar sun kashe ‘yan ta’adda 974 tare da kama wasu 621 a cikin watan Fabrairu, 2024.

Rundunar sojin ta kuma ce ta kubutar da mutane 466 da aka yi garkuwa da su a cikin wannan lokaci da ake shirin karbar kuɗin fansa.

Daraktan yada labarai na tsaro Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce an kashe ’yan ta’addan ne a lokacin da aka yi musayar wuta tsakanin sojojin kasa da sojojin sama a yankunan ‘yan ta’addan.

Kakakin rundunar tsaron ya ce sojojin sun kwato makamai iri-iri 1,573, alburusai iri-iri 23,345 tare da hana barayin man fetur satar man da aka kiyasta kudin shi ya kai N8,006,996,894.00 a tsawon lokacin.

Ya bada jimlar kayayyakin da aka kwato kamar haka: “Bindigu AK-47 640, bindigogi kirar gida guda 248, bindigogin toka guda 93, bindigogin dane guda 168, zagaye na harsashi 15,120 na 7.62mm na musamman ammo, zagaye na harsashi 6,102 na 7.62mm NATO, zagaye na harsashi 512 na 9mm.

“Sauran sun hada da lita 8,993,245 na danyen mai da aka sace, lita 1,062,635 na AGO da aka tace ba bisa ka’ida ba, lita 18,950 na DPK da lita 45,950 na PMS da dai sauransu.”

Da yake karin haske, Janar Buba ya ce an kashe fitattun jagororin yakin ‘yan ta’adda a lokacin da sojojin na Operation HADARIN DAJI ke fafatawa da su.

“Ashiru SHIRU da Kachambi, dukkansu masu biyayya ga Jimmo ‘Smally’ an kashe su ne a farkon ranar 24 ga watan Fabrairu da sojoji tare da ‘yan banga a kusa da Faru, karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara” in ji shi.