Ronaldo Ya Sayar Da Takalmin Zinaren Shi, Ya Baiwa Falasdinawa Kudin

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya bayar da gudunmuwar Yuro miliyan €1.5 ga yaran Falasdinawa a Gaza, kamar yadda kafar yada labarai ta Classico ta larabci ta bayyana, jaridar Russia Today ta ruwaito.

An ta yaɗa sakonnin yabon Ronaldo da yawa a shafukan sada zumunta bayan rahotannin, Ronaldo ya siyar da tsaloffin takalman shi na zinare (Golden Boot), kuma ya bayar kuɗin tallafin ga mutanen Gaza da cikin tsananin bukatar taimako a wannan mawuyacin hali.

Ba Ronaldo ne kadai ke nuna goyon baya ga Gaza ba, kamar yadda Adem Sarı na Samsunspor ya sanya rigar rigar da aka rubuta “Yanci ga Falasdinu”.An

An bayyana cewa ya sayar da takalmin akan kuɗi kimanin Yuro miliyan dubu ɗaya da rabi (€1.5).